“Saboda bakin Karuwancin da Matata ke yi har hawan jini ne ya Kamani” – Magidanci ya nemi kotu ta raba Aurensu.

Kotu

Justine Onu wani magidanci kuma da kasuwa ya roki kotu da ke zamanta a Jikwoyi, garin Abuja da ta taimaka ta datse igiyar aurensa da matara Joyce.

Magidan ya bayyana cewa saboda tsabar bakin mugun halin matar tasa ya sa ya kamu da hawan jini.

Bakin halin matar tasa shi ne karuwanci. Onu ya ce matarsa ta canja kwata-kwata daga yadda ya aureta.

“ Karuwacin matata ya yi tsanani matuka abin ya kai ga hatta ɗan uwanta tana kwana da shi. Ni na da kai na kamata turmi da taɓarya tana zina da ɗan uwanta a gida na. Yaya za a ce zuciyata ba zata ta buga ba, hawan jini ya kama ni.

Kamar yadda jihar PremiumTimes Hausa ta ruwaito, Mr. Onu ya ce matarsa bata da dabaran yadda za ta iya tafiyar da harkokin cikin gidanta yadda ya kamata a matsayinta na matar aure.

” Matata sam bata iya kula da gida ba. Komai nata a yamutse suke babu kan gado. Sannan kuma ga ɓarnata abinci babu tattali. Duk abinda ka bata za ta kashe su.

“Sannan gashi ko iya kula da ‘ya’yan ta ma ba ta iya ba. Dukundukun zaka rika ganin su.

Sai dai kuma Joyce to musanta duka korafin da mijin ya faɗi a kanta

Alkalin kotun Labaran Gusau ya ce za a ci gaba da shari’ar ranar 9 Faburairu.

HED Desk 286 Posts
We are who we are and we are specialized in what we do. This is HED Desk and our main aim is to provide fresh, unique and, of course, legit content to our beloved users on a daily basis. For more info email us: [email protected] or Whatsapp Us: +2348120004644.

Drop Your comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*