Kimanin Mutum Miliyan Takwas Sun Tsere Daga Ukraine – Inji Majalissar Dinkin Duniya

Ukraine

Jami’in bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya Martin Griffiths a ranar Talata ya ce kusan mutane miliyan takwas ne suka tsere daga Ukraine tun farkon fara rikicinta da Rasha kusan shekara guda da ta wuce.

A cewar Griffiths, kusan mutane miliyan takwas ne suka tsere daga Ukraine zuwa kasashe makwabta, yayin da wasu miliyan 5.3 ke gudun hijira.

Shugaban ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, ya ce mutane miliyan 17.6, wato kusan kashi 40 cikin 100 na al’ummar Ukraine, na bukatar agajin jin kai.

Griffiths ya ce ya yi niyyar gabatar da shirin ba da agajin jin kai na bana ga Ukraine, wanda ke bukatar dala biliyan 3.9 a Geneva a karshen wannan wata.

“Wannan tashin hankalin ba ya nuna alamar raguwa,” in ji shi.

Alkaluman hukumar MDD sun ce sama da fararen hula 7,000 ne aka kashe tun bayan da Rasha ta fara mamaye kasar Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022.

“Hakika adadin ya fi girma,” in ji Griffiths.

A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, yakin da Rasha ta yi da Ukraine ya kai ga gudun hijira mafi girma tun bayan yakin duniya na biyu

HED Desk 286 Posts
We are who we are and we are specialized in what we do. This is HED Desk and our main aim is to provide fresh, unique and, of course, legit content to our beloved users on a daily basis. For more info email us: [email protected] or Whatsapp Us: +2348120004644.

Drop Your comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*