Gwamnatin Masari ta ayyana gobe ranar hutu ga ma’aikata don su tarbi Buhari

Aminu Bello Masari

Yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zo jihar Katsina gobe, Gwamnatin jihar Katsina ta ayyana ranar 26 ga watan janairu a matsayin ranar hutu ga dukkanin ma’akatan kananan hukumomin jihar.

Haka na kunshe ne cikin wata sanarwa Alhaji Sani Kabomo babban sakataren ma’aikatar noma da walwalar jama’a na jihar ya fitar ga manema labarai a yau Laraba.

Kobomo ya ce gwamnatin jihar ta bai wa ma’aikatan hutu ne don su samu lokacin yin shirin tarbar shugaban kasa Muhammadu Buhari a wata ziyara da zai kai jihar don kaddamar da wasu ayyukan da Masari ya kammala.

Ya kuma kara da cewa, hutun sam bai shafi wadanda suke aiki karkashin gwamnatin tarayya, bankuna da ayyuka na musamman ba.

Abba Abdullahi Garba 245 Posts
Life is simple it depends on the way you take it, the art of simple life is to be simple. For info, enquiries or requests mail me at: [email protected]

Drop Your comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*